- Malaman kimiyya sun gudanar da bincike kuma sun gano cewa aje mage a gida na kara karsashin zamantakewa
- Akwai alamun da ke bayyana cewa akwai alakar zamantakewa tsakanin mage da mutum wanda aka gano a tsibirin Cyprus
- Akwai maguna masu kyau kamar nau'in Van dake kusa da tafkin kasar Turkiyya
Malaman Kimiyya da suka gudanar da bincike kan alaka dan Adam da dabbobi, sun gano cewa kiwata mage na kara wasu abubuwa da dama ga lafiyar dan adam. Zama da mage a gida na kara karsashin zamantakewar mutum tare da kara yawan yin dariya da motsa jiki wanda ke rage damuwa. Hakan na kara karfin garkuwar jikin dan Adam.
Daya daga cikin shaidun dake tabbatar da alakar mage da dan adam shi ne kwarangwal din wata mage mai shekaru dubu 9,500 dake tsibirin Cyprus wanda aka yi amfani da jirgin ruwa wajen kaita da muzuru 1 zuwa tsibirin wanda a lokacin babu mage a cikinsa. Wannan na nuna cewar a yankin Anadolu shekaru dubu 10,000 da suka gabata ana rayuwa tare da mage.
KU KARANTA: Nesa ta zo kusa: Nnamdi Kanu zai shigo Najeriya jana'izar iyayensa wata mai zuwa
Daya daga cikin maguna masu kyau ita ce nau’in Magen Van wadda ke rayuwa a kusa da tafkin Van na Turkiyya. Wannan mage na da idanuwa ruwan shudi da ruwan zuma wanda ake ganin lalacewar ido ne. Tana da farar jela mai kama da ta dila da kuma gashi mai ba sha’awa. Tana son ruwa tare da kaunar ninkaya.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng
ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHB9kXJramphYq6ussCnoKdlm57EsLqMppignV2Weqi1w5pkoJldosK1rc2eZaGsnaE%3D